Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi a Nijer


A yau Lahadi 13 ga watan Disamba ake gudanar da zaben kananan hukumomi a Jamhuriyar Nijer da nufin samar da mutanen da zasu wakilci al’umma a majalisun jihohi da na da’irori.

Shugaban Nijer Issouhou Mahamadou ne ya bada izinin wannan zabe bayan da ya kada kuri’arsa da hantsi a cibiyar zabe ta 1 da ke ma’aikatar magajin garin Yamai, ya kuma yaba wa hukumar zaben ta CENI akan samun wannan nasara tare da yin kira ga ‘yan kasa su fito don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu cikin nutsuwa.

Shugaban Nijar Issouhou Mahamadou zai kada kuri'arsa
Shugaban Nijar Issouhou Mahamadou zai kada kuri'arsa

Shugaban ya kara da cewa aiki ne mai matukar wuya amma hukumar CENI ta tsara zaben cikin kankanen lokaci, bayan haka ya kuma jinjina wa jam’iyyun siyasa saboda yadda suka gudanar da yakin zabensu cikin kwanciyar hankali ya kuma bukaci su ci gaba da nuna irin wannan halayya a yayin yakin neman zaben ‘yan majalisar dokokin kasa da na shugaban kasa da ke tafe.

Shugaban Nijar Issouhou Mahamadou ya kada kuri'arsa
Shugaban Nijar Issouhou Mahamadou ya kada kuri'arsa

Kimanin ‘yan Nijer miliyan 7 da kusan rabi da suka yi rajista ne ake sa ran zasu fito a tsawon wunin ranar Lahadi domin kada kuri’a a zaben na kananan hukumomi da ke matsayin na share fagen babban zaben kasar.

Nafou Wada, kakakin hukumar zaben, ya tabbatar da cewa hukumar ta CENI ta aike da kayan zabe zuwa dukkan sassan kasar sai dai an samu tsaiko a wasu wuraren saboda wasu dalilai.

Wasu daga cikin masu zabe sun nuna damuwa a game da rashin daukar matakan kare kai daga annobar COVID-19 a rumfunan zabe a yayin da alkaluman hukumomin kiwon lafiya ke nunin cutar na ci gaba da yaduwa.

A karfe 7 na yamma ne za a rufe runfunan zabe, to amma shugabannin hukumar CENI sun ce, za a ci gaba da kada kuri’a a rumfunan da aka fuskanci tsaiko har lokacin da zasu cike wa’adin awoyi 11 kamar yadda ya ke rubuce a kundin zaben kasar na Code Electorale.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00


XS
SM
MD
LG