Nouhou Mahamdou Arzika, shugaban ofishin kungiyar MPCR da wasu masanan doka irinsu Pr Djibril Abarchi ne suka shirya wata mahawarar bainar jama’a domin fadakar da mazaunan birnin Yamai muhimancin zabe da kuma irin abubuwan da ya kamata talakawa su yi la’akari da su, kafin su bai wa jam’iyyun siyasa kuri’unsu ranar zabe don kaucewa zaben tumun dare.
A nata bangaren kungiyar REJEA mai fafitikar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, a yayin zaman hadin gwiwar da suka shirya da kungiyar Water Aid, sun maida hankali wajan jan hankalin ‘yan takara akan maganar samar da ruwan sha ga al’umma, a cewar Malam Ousman Dambaji, shugaban kungiyar.
Tun a shekarar 2015 ne wa’adin kansiloli, da magadan gari, da na ‘yan majalisun jiha ya kammala a hukumace, amma wasu matsaloli da suka gitta suka hana a shirya zaben da zai bada damar sabunta wadannan majalisun, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin Nijer kirkiro da dokar karin wa’adin a kowane wata 6. Saboda haka zaben na ranar Lahdi 13 ga wata ke da muhimmanci a wajen talakawan kasar.
Kawo yanzu dai komai ya kammala game da tsare-tsare, saboda haka za a gudanar da zabe ba tare da fuskantar wata mishikila ba a cewar hukumar zabe ta CENI.
Saurari cikakken rohoton Souley Moumouni Barma: