Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Cire Sudan Daga Jerin Kasashen Da Ke Daukar Nauyin Ta'addanci


Janar Abdel-Fattah Burhan.
Janar Abdel-Fattah Burhan.

Janar Abdel-Fattah Burhan, shugaban gwamnatin hadin gwiwar Sudan, ya yaba da matakin na gwamnatin Trump a matsayin na tarihi.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Khartoum ya fada a yau Litinin cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump ta cire kasar Sudan daga jerin kasashen da Amurka ta sanya a matsayin kasashen da ke daukar nauyin ta’addanci, wani mataki da ta yiwu ya taimaka wa kasar ta nahiyar Afrika samun bashi daga kasashen duniya don farfado da tattalin arzikinta da ya tabarbare, ya kuma kawo karshen maida ta saniyar ware.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Khartoum ya fada a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa matakin kan Sudan zai fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Disamba, kuma za a wallafa sanarwar matakin, wadda sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanya wa hannu a takardun gwamnatin Tarayya da ake wallafawa.

Sanya Sudan a matsayin kasa mai daukar nauyin ta’addanci ya fara ne tun a shekarun aluf dari tara da cisi'in da wani abu, lokacin da Sudan ta karbi bakuncin jagoran kungiyar al-Qaida Osama bin Laden da wasu mayaka da ake nema ruwa a jallo, na wani dan lokaci. An kuma yi imanin cewa Sudan ta kasance kasar da aka yi amfani da ita don Iran ta sama wa mayakan Falasdinu makamai a yankin Zirin Gaza.

Cire Sudan daga jerin kasashen da ke daukar nauyin ta'addanci wani muhimmin matakin karfafa gwiwa ne ga gwamnatin Khartoum don ta daidaita dangantakarta da Isra’ila. Kasashen biyu sun amince su samu cikakkiyar dangantakar diflomasiyya, abinda ya sa Sudan ta zama kasar Larabawa ta uku bayan Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, da suka dauki matakin gyara dangantakarsu da Isra’ila a bana.

Karin bayani akan: Amurka, Buhari, da Shugaba Donald Trump​.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG