A cikin wata sanarwa ce da ma’aikatar harakokin wajen kasar Jamus ta fita inda ta ce kasar zata rufe sansanin sojojinta dake Nijar a ranar 31 ga watan Augusta mai kamawa bayan da kasashen biyu suka kasa cimma matsaya kan tsarin bayar da horo da kuma makamai.
Sansanin na zaman wata hanyar yakar ta’addanci ne a kasashen yankin Sahel karkashin kulawar majalisar dinkin duniya.
Sai dai masana harakokin yau da kullun irinsu Abdurahmane Dikko na ganin ficewar dakarun kasar Jamus daga Nijar ba zai rasa nasaba da sabuwar alakar dake tsakanin Nijar da kuma Rasha ba.
Wannan matakin na Jamus ya kara jaddada irin tsamin dangantaka dake tsakanin kasashen yamma da kuma hukumomin mulkin sojin Nijar, to sai dai Alkassoum Mato masanin harakokin tsaro a Nijar ya bayyana dalillan da suka sanya Jamus daukar wannan matakin na ficewa daga kasar Nijar akan batun shigar Rasha kasar ne.
A lokutan baya dai Jamus ta bukaci kulla yarjejeniya ta wucin gadi da kasar ta Nijar ne, sai dai ga dukkan alamu ficewar dakarun kasashen Faransa da Amurka daga Nijar ya kawo cikas ga kasasncewar Jamus a wannan kasa ta yankin Sahel.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna