Alhaji Tanko Yakasai yayi furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a garin Kaduna lokacin da yake kaddamar da kwamitin amintattu na majalisar dattawan arewa.
Shugaban yayi watsi da zargin da ake yiwa majalisar cewa ta sharewa shugaba Jonathan faggen zaben 2015 ce. Yace shi bashi da tsoron zaben badi domin tun daga 1951 yake ganin ana yin zabe. An saba da yin hayaniya ya kuma wuce sabili da haka zabe mai zuwa ba zai zama daban ba. Yace kada wani dan kasa ya yadda a yi anfani dashi ya tada hankalin kowa.
Tsohon sifeton janaral 'yansandan Najeriya Alhaji Muhammed Gambo Jimeta shi ne shugaban kwamitin amintattun majalisar. Shi ma yace ba suna yi ba ne domin Jonathan ba. Suna yi ne domin kasar akan halin da mutanen arewa suke ciki. 'Yan arewa ne suka fi cutuwa, su ne suka fi talauci, su ne kuma suka fi samun tashin hankali. Duk wanda zai kawo zaman lafiya, ya fitar da mutanen arewa daga cutarwa zasu mara masa baya.
Duk da kokarin nisanta majalisar daga shugaban kasa tsohon shugaban PDP kuma tsohon ministan tsaro Alhaji Muhammed Bello Haliru yace ba zasu yaki shugaba Jonathan ba ko wani shugaba da ya fito daga wata jiha da ba ta arewa ba. Ba arewa kadai bace Najeriya. Ta hada da jihohin kudu da arewa. Hadin kan Najeriya ba zai yiwu ba sai an hada da kowa da kowa. Ba zasu yi fada da kowa ba ko akan kabila, siyasa ko addini. Bisa ga abubuwan da shugaban kasa ke cewa sun gamsu za'a yi zabe nagari.
Ganin yawan 'yan jam'iyyar PDP a majalisar, wakilin Muryar Amurka ya tambayi daya daga cikin 'yan majalisar Sanata Ahmed Mukhtar Aruwa shin ko basa ganin za'a daukesu a matsayin reshen jam'iyyar PDP. Yace kungiya ce ta arewa. Kowa na iya shiga cikinta. Ba'a hana kowa ba.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.