Sakatarorin sun fito ne daga duk fadin Najeriya suka taru a Legas.
Taron shi ne na farko da wata jam'iyya zata shirya wa sakatarorin yada labaranta. Masu shirya taron sun ce sun shirya taron ne domin musayar ra'ayoyi game da yadda zasu yi nasara a zabe mai zuwa.
Bayan taron sun ce zasu samar da wani matakin musayar ra'ayi musamman a jihohin da ba jam'iyyarsu ke mulki ba domin su yi tasiri a zabe mai zuwa cikin ruwan sanyi.
Daya daga cikin mahalartan taron Alhaji Sani Gwamna daga jihar Zamfara yace bayan waye wa masu jefa kuri'a kai zasu gane matsalolin junansu tare da baiwa junansu shawara. Da wakilin Muryar Amurka ya tambayeshi ko duk abun da suke yi zai yi tasiri domin siyasar Najeriya sai da masu gidan rana kuma su basu rike da masu gidan rana amma sai yace ta hadin kan da suka fara ta haka zasu samu nasara ta wayar da kan jama'a musamman ganin irin halin da ake ciki yanzu.
Injiniya Bashir Yahaya Karaye sakataren yada labarai na jam'iyyar a Kano yace ko bayan wayar da kan jama'a suna son su sani shin ina jam'iyyarsu ta kwana. Ina take yanzu a siyasar Najeriya. Taron zai basu damar kaiwa uwar jam'iyyarsu ta san nasarorin da wasu jihohi suka samu.
Da aka ce masa ke nan shugaban yada labarai na kasa na jam'iyyar ya kasa cimma muradunsu shi yasa suka shirya taron domin su yi masa tallafi sai yace ko kusa ba haka maganar take ba. Yace shugaban yada labarai na jam'iyyar na kasa yana iyakacin kokarinsa. Yace tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadi samun sakataren yada labarai na kasa, na jiha, na kananan hukumomi da na mazaba. Jam'iyyarsu tana son a yi kowane abu bisa ka'ida.
Sakataren jihar Bayelsa da aka tambayeshi yadda jam'iyyar zata iya yin tasiri a jihar da shugaban kasa ya fito sai yace shugaban jam'iyyarsu tsohon gwamnan jihar dan siyasa ne mai hulda da talakawa kuma mutum ne wanda baya kyamar mutane. Mutane suna tururuwa suna shiga jam'iyyar lamarin da ya nuna mutanen Bayelsa suna bukatan canji.
Taron zai duba nasarori da matslolin jam'iyyar a duk fadin kasar. Taron zai zame matakin farko kan yadda zasu tunkari zabe mai zuwa.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.