Kodayake shugaban kawo yanzu bai fito fili yace zai sake tsayawa zabe ba amma ana harsashen yana kwadayin yin hakan ganin yadda aka tayin fafitika a kotu tsakanin mutanensa da wadanda basa son ya sake tsayawa.
A tattaunawar da wakilin Muryar Amurka yayi da mataimakin sakataren wasa labarai na jam'iyyar PDP Barrister Abdullahi Jalo yace bayanan da ake yi dangane da tarurukan da ake gani, taruruka ne na kungiyoyi masu zaman kansu da suka sa kai ba wai PDP ba ce ko gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta shiryasu ba.
Yace kungiyoyi da ake kira NGOs kamar su Transformation Ambassadors kamar wadda shi yake ciki Housa to House da wasu kungiyoyi na kasa suke shirya tarurukansu su gayyaci wanda suka ga dama.
Wakilin Muryar Amurka yace masa kungiyoyin suna buga hoton Jonathan suna fadar ranakun da zai yi jawabi, to kenan shirye-shirye ne na neman zabe a labe domin kada a fito fili a fadawa jama'a ainihin manufar tarurukan. Ana anfani da NGO ne domin ya samu hurumin yin tsarin. To saidai Barrister Jalo ya mayar da martani inda ya tambayi wakilin Muryar Amurka ko ya ga shugaban PDP na kasa awurin taron ko wasu jigajigan jam'iyyar.
Barrister Jalo ya kara da cewa kungiyar Transformation Ambassadors NGO ce kuma zata je Maiduguri jihar Borno ta taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu su kuma basu gudummawa.
A waje daya wani kusa a jam'iyyun adawa Alhaji Musa Bukar yana ganin cewa lallai maganar kemfen tuni an riga an fara kuma gwamnati da fadar shugaban kasa suna da hannu dumu-dumu a cikin al'amarin. Yace su kungiyoyin da ake cewa NGOs ne masu zaman kansu suna yin layi a ofishin kemfen din Jonathan ana basu kudi. Mutanen gwamnati ke baiwa kungiyoyin kudi suna tallatar da Jonathan.
Da wakilin Muryar Amurka ya cewa Alhaji Bukar cewa kungiyoyin basu fadi sunan jam'iyya ba su dai suna ganin shugaban yayi wasu ayyuka masu kyau da yakamata mutane su sani, sai yace wakilin Muryar Amurka ya je ofishin jam'iyyar PDP zai ga kungiyoyin sun yi layi suna bada lambobin asusunsu da sunayen bankunansu. Domin menene suke yin hakan.
Ga cikakken rahoto.