Manufar ganawar tasu shi ne yadda za'a samo bakin zaren warware matsalar da ta addabi kasar ta fuskar tsaro lamarin dake neman durkusar da darajar Najeriya a gida da waje.
Ganawar tazo da bazata saboda an dade da tsohon shugaban ya baiwa shugaba Jonathan shawarwari akan yadda za'a kawo karshen fitinar 'yan Boko Haram da kuma irin takunsakar da aka yi sabili da wasu wasiku da shi Olusegun Obasanjo ya rubuta akan lalacin da yake gani na tattare da gwamnatin Jonathan.
Abun mamaki sai gashi shugaba Jonathan ya gayyato Olusegun Obasanjo domin tuntubar juna akan yadda za'a warware matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Kodayake fadar gwamnati bata ce uffan ba akan ganawar amma shi Obasanjo ya bayyanawa manema labaru cewa sun yi ganawar bisa ga gayyatar da ya samu daga shugaban kasa. Sun tattauna sha'anin tsaro kuma bayan batun tsaro babu wata magana kuma da suka yi. Ya kuma bada tabbacin cewa idan gobe aka sake gayyatoshi domin a warware matsalar Najeriya ashirye yake ya bada shawara.
Wasu masu harsashen harkokin yau da kullum suna ganin maganar da suka yi ta wuce ta tsaro har ma ta shiga ta siyasa kamar yadda Malam Husseni Mongunu ya shaida. Yace batun Boko Haram akwai siysa ciki sabili da haka babu yadda tsohon shugaban kasa irin Obasanjo yayi maganar tsaro bai tabo batun siyasa ba. Yace lokacin da aka sace daliban Chibok Obasnajo ya tada wadanda ke iya ganin 'yan Boko Haram. Sun je kuma sun gana da shugabannin kungiyar. Sun tattauna sun kuma koma sun ba Obasanjo rahoton ganawarsu. Shi Obasanjo ya shaidawa shugaba Jonathan abun da ya faru ya kuma bada shawara amma shugaba Jonathan ya sa kafa ya ture maganar.
Obasanjo ya ba shugaban kasa shawara akan yadda za'a tunkari tsagerancin 'yan Boko Haram amma wadanda suke kewaye da shugaban suka hanashi yin anfani da shawarar tsohon shugaban kasar.Maganar cin hanci da rashawa tayi katutu a maganar Boko Haram. Misali gwamnati na bada kudi a sayi kayan yaki amma yau sojojin kasar basu da bindigogin da zasu tunkari 'yan Boko Haram. Yadda sojojin Najeriya 480 suka arce zuwa kasar Kamaru ya nunawa shugaban cewa abun da hafsoshinsa ke fada masa da walakin a a ciki dalili kenan ya nemi ganawa da Obasanjo da nufin komawa kan shawarwarin da ya bayar da can. Yanzu shugaban yana son ya ji gaskiya ba karerayin da aka dabaibayeshi dasu ba da.
Ganawar tana da mahimmancin gaske wurin kubutar da sojojin Najeriya daga irin halin da suka shiga ko suka samu kansu a hannun 'yan Boko Haram. Yanzu dai an ce rashin kayan aiki da makamai yasa sojojin suna shakkar tunkarar 'yan kungiyar.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.