ACCRA, GHANA - Jama'ar Ghana na ganin ana jinkiri wajen aiwatar da dokar kama masu luwadi da madigo, mafi yawancin sun yi kira da gwamanati da ta gaggauta aiwatar da dokar.
Hon. Muntaka Mubarak Mai wakiltan mazabar Asawase kuma tsohon shugaban masu ladabtar wa a Majalisa ya ce an kai bangare na biyu wajen aiwatar da dokar saura bangarori biyu kafin zantarwa.
Kakakin Majalisar Dokokin Ghana Alban Sumana Kingsford Bagbin yayin da yake baiwa membobin Majalisar Dokokin damar bayyana ra’ayinsu ya bukaci duk dan Majalisar da bai goyi bayan dokar ba ya tashi tsaye domin bayyana dalilansa na kin amincewa.
Bisa ga tsarin dokar dai da ake shirin aiwatar wa a Ghana, za'a daure duk wadanda aka kama da laifin luwadi ko madigo da zama gidan yari har na tsawon shekaru goma, sannan shekaru uku kuma ga duk wanda ya bayyana yanayin luwadi ko madigo.
Saurari cikakken rahoton Hauwa AbdulKarim:
Dandalin Mu Tattauna