Yayin da yake kasar Uganda, Raisi ya ce kasashen Yamma suna tallata luwadi da madigo domin kawo karshen abin da ya kira “makomar zuri’ar dan Adam”.
Ziyarar ta Raisi ta zo ne bayan a watan Mayun da ya gabata Uganda ta rattaba hannu kan wata doka mai tsauraran hukunce-hukunce kan ‘yan luwadi da madigo ciki har da hukuncin kisa.
A lokacin ziyararsa ta yini guda a Uganda a wannan makon, Raisi, wanda ke magana ta bakin tafinta, ya bayyana luwadi da madigo a matsayin wani hari da ke adawa da tubalin gina zuri’a da gado, fanin da a cewarsa, Uganda da Iran za su iya yin hadin gwiwa.
"Kasashen Yamma suna ƙoƙarin maida luwadi a matsayin alamar wayewa, yayin da wannan yana ɗaya daga cikin batutuwa mafi ƙazanta," in ji shi.
Raisi ya yi wannan tsokaci ne domin nuna goyon bayansa ga matakin da Uganda ta dauka na abin da aka bayyana a matsayin daya daga cikin dokoki mafi tsauri a duniya kan 'yan luwadi.
Dokar, wacce aka zartar a watan Mayu, ta sanya hukuncin kisa kan masu aikata luwadi da kuma hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saboda tallata aikin. Matakin ya sa wasu 'yan kasar Uganda tserewa zuwa makwabciyar kasar Kenya.
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana matakin a matsayin "bai dace ba" da kuma "abin kunya ne."
Wani mai fafutukar kare hakkin bil adama Frank Mugisha ya ce: "Suna ci gaba da cewa kasashen Yamma suna tura akidunsu kan Uganda, amma duk da haka muna da wasu kasashe masu tsoma baki tare da ingiza nasu kimar a Uganda," in ji shi. "Alal misali, Iran - mun san suna goyon bayan kungiyoyi masu adawa da luwadi a nan kasar."
Mugisha ya ce tun lokacin da aka kafa dokar haramta luwadi, ‘yan luwadi sun fuskanci cin zarafi da dama daga masu ba da hayar gidaje da kananan hukumomi.
Ziyarar da Raisi ya yi a wasu kasashe uku na Afirka wani yunkuri ne na bunkasa alakar diflomasiyya ta Iran da nahiyar.
Dandalin Mu Tattauna