Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban EFCC Ya Ce Zasu Daukaka Kara Bisa Hukuncin Wata Babbar Kotun Najeriya


Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC.
Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC.

Wata babbar kotun birnin tarayya ta yankewa Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC hukuncin zama a gidan kaso sabili da gazawar hukumarsa na kin bin umarnin kotu na baya.

Shugaban na hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa, hukumarsa zata daukaka kara a bisa hukuncin wata babbar kotun tarayya dake da zama a birnin Abuja, da ta ce ta tura shugaban EFCC gidan gyara hali na Kuje a bisa laifin rashin biyayya ga hukuncin kotun da ta ce a mayar wa wani mutum wasu kudadde da motorsa.

Bawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ta wayar tarho ga Muryar Amurka a game da labarin aika shi kurkukun Kuje da ya karade kafaffen yanar gizo yana mai cewa, ba shi ne shugaban hukumar EFCC ba a lokacin da lamarin ya faru a shekarar 2018 ba.

Ofishin EFCC a Abuja
Ofishin EFCC a Abuja

A wani hukunci da ta yanke a ranar Talata, mai shari’a Chizoba Oji ta bayyana cewa shugaban hukumar EFCC na lokacin, ya yi watsi da umarnin da kotun ta bayar a ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2018, inda ta umurci hukumar da ta mayar wa wani mai mota kirar Range Rover kayan shi ta kuma biya shi Naira miliyan 40.

Jami'an Hukumar EFCC suna karbar horo
Jami'an Hukumar EFCC suna karbar horo

Mai shari’a Oji ta kuma umurci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, da ya tabbatar da cewa an aiwatar da umurnin kotun nan take.

Haka kuma mai shari’ar ta ki amincewa da hujjojin da lauyan hukumar EFCC, Francis Jirbo, ya gabatar.

Hukuncin da aka yanke a ranar 28 ga watan Oktoba, wanda gidan Talabijin na Channels ya gani, yana kan wani kudiri ne bisa takardar sanarwa da Air Vice Marshal (AVM) Rufus Adeniyi Ojuawo, wanda ya taba zama Daraktan Ayyuka a Najeriya ya shigar.

Saurari cikakken rahoton Halima AbdulRauf:

Shugaban EFCC Ya Ce Hukumarsa Za Ta Daukaka Kara A Bisa Hukuncin Wata Babbar Kotun Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00

XS
SM
MD
LG