Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu ta Yanke wa Wani Mutum Hukuncin Shekara 28 A Gidan Yari Saboda Damfara - EFCC


Ofishin EFCC a Abuja
Ofishin EFCC a Abuja

Tuhume-tuhume sun hada da alaka da samar da takardun bogi, hadin baki da zambar kudi ta Naira miliyan 39.

Mai shari’a Akintayo Aluko na babbar kotun tarayya dake abakaliki, jihar Ebonyi, ya yanke wa Emeka Anaga hukuncin shekaru 28 a gidan gyaran hali bayan da hukumar EFCC ta gurfanar da shi akan tuhume-tuhume 38.

Tuhume-tuhume sun hada da alaka da samar da takardun bogi, hadin baki da zambar kudi ta Naira miliyan 39. A ranar Alhamis ake yankewa Anaga wannan hukunci a cewar EFCC.

“An tuhumi wanda aka yanke wa hukuncin da zambatar wani mai suna Innocent Nwachukwu da aka fi sani da Inno Maiduguri, dan kasuwa akan ya biya shi Naira miliyan daya inda ya masa alkawarin sama mishi kwangila daga kamfanonin wayar sadarwa a jihohin Ebonyi, Delta, da Kano.” Hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a.

Anaga ya musanta laifin da aka tuhume shi da shi sai dai bayan kotu ta saurari karar, mai shari’a ya kama shi da laifi akan tuhuma 34 inda ya yanke masa shekaru goma saboda laifin hadin baki da wasu shekaru goma sha biyu saboda zamba.

Haka ma mai shari’a ya yanke masa hukuncin shekaru takwas saboda zamban kudi Naira dubu 973, 000.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG