Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Kama Mutum 92 Da Take Zargi Da Ayyukan Damfara Ta Yanar Gizo


Mutanen da EFCC take tuhuma da laifukan damfara ta yanar gizo (Hoto: Facebook/EFCC)
Mutanen da EFCC take tuhuma da laifukan damfara ta yanar gizo (Hoto: Facebook/EFCC)

Hukumar ta EFCC ta ce ta samu nasarar cafke mutanen ne a birnin Fatawkal wadanda ake kira “Yahoo Boys,” bayan wasu bayanan sirri da ta tattara.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon kasa a Najeriya, ta ce ta yi nasarar cafke mutum 92 wadanda take zargi da gudanar da ayyukan da suka shafi damfara ta yanar gizo a birnin Fatakwal na jihar Rivers da ke kudancin kasar.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a ta ce, da sanyin safiyar ranar Laraba, jami’anta suka yi wa mutanen dirar mikiya a wurare daban-daban na jihar ta Rivers.

“Mun kama mutum 92 da ake zargi da aikata ayyukan damfara a wuraren da suka hada da Choba da Ada George a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers.” Sanarwa ta ce.

Hukumar ta EFCC ta ce ta samu nasarar cafke mutanen ne wadanda ake kira “Yahoo Boys” bayan wasu bayanan sirri da ta tattara.

Ta kara da cewa, na’urorin da aka kwace a hannun mutanen da ake zargin, sun nuna cewa 64 daga cikin mutum 92 na da hannu dumu-dumu a ayyukan na damfara.

A wani labari makamancin wannan, hukumar ta EFCC ta ce ta kuma kama wasu mutane 39 a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke kudancin Najeriya, wadanda su ma take zarginsu da ayyukan damfara ta yanaar gizo.

TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yaki Da Matsalar Almajiranci A Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG