Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neman Sassaucin Da Tsohon Babban Akantan Najeriya Ya Yi Ya Gamu Da Cikas


EFCC
EFCC

Hukumar EFCC ta yi karin haske kan rashin cimma matsaya tsakanin bangaren hukumar da dakataccen babban akanta janar na tarayyar Najeriya a game da bukatar neman sassauci a maida kudadden da ake zargin ya wawure ga lalitar gwamnat don a rage tsaurin hukuncin kotu da ake kira "plea bargain."

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta bayyana cewa babban akanta janar na Najeriya da aka dakatar a bisa zargin almundahanar Naira biliyan 109, Ahmed Idris, da wasu mutane uku sun fara yunkurin neman sassauci da ake cewa "plea bargain" a turance, a wajen EFCC don rage tsaurin hukuncin da kotu zata iya zartarwa a kan su idan aka tabbatar da cewa sun aikata laifin.

Babban lauyan wadanda suka shigar da kara wato EFCC, Rotimi Jacobs mai mukamin SAN dai ya ce Idris ya tuntube shi ta hannun wani mutum na daban domin ganawa kan hanyoyin da za a bi wajen cimma matsayar neman sassauci a matsayin mafita, lamarin da ya fuskanci tsaiko sakamakon kin zuwa da lauyoyin bangaren Akanta Idris suka yi bayan amincewa da haka a bisa doka da kuma yarjejenuta da wakilin EFCC.

Idan ana iya tunawa, a ranar 22 ga watan Yuli ne aka gurfanar da dakataccen babban akanta Janar Ahmed Idris, Mataimakinsa a sashen aiki, Godfrey Olusegun Akindele, wani darakta a ofishinsa, Mohammed Kudu Usman, da wani kamfani mai alaka da Idris wato Gezawa Commodity Market and Exchange Limited a gaban kotu a kan tuhume-tuhume 14 da suka hada da almundahanar Naira biliyan 109, sata da kuma cin amana wajen sauke nauyin aiki.

A ranar laraba 9 ga wannan watan na Agustan ne babbar kotun tarayya dake Abuja ta dage zaman sauraron shari’ar Ahmed Idris da sauran wadanda ake tuhuma zuwa ranar 4 ga watan Oktoban shekarar nan don ci gaba da sauraro har a kai ga zartar da hukunci da ya dace Idan aka kama su da laifi.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Neman Sassaucin Da Tsohon Babban Akantan Najeriya Ya Yi Ya Gamu Da Cikas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:26 0:00

XS
SM
MD
LG