Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Dakatar Da Yarjejeniyar Cinikayya Da Koriya ta Kudu


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Trump ya yi barazanar dakatar da yarjejeniyar cinikayya da ya cimma da kasar Koriya ta Kudu kwanaki biyu da suka wuce wadda shi da kansa ya kira "nasara ga ma'aikatan kasashen biyu"

Kwana daya bayan da ya kira yarjejenyar cinikayya tsakanin Washington da hukumomi dake birnin Seoul, a zaman "nasara ga ma'aikatan Amurka da Koriya" shugaba Donald Trump, ya yi barazanar dakatar da fara aiki da sabauwar yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu.


Trump ya fadawa wani taro jiya Alhamis a jihar Ohio, cewa tana yiwuwa ya fasa aiwatar da wannan yarjejeniya, har sai bayan an cimma yarjejeniyar wargaza makaman nukiliyar Korea ta Arewa.


Ya kira sabunta yarjejeniya da Korea ta Kudu muhimmin batu kuma yace zai tabbatar da ganin an yiwa kowa adalci.


Trump bai yi karin bayani a kan dabarunsa na dakatar da yarjejeniyar ko kuma wane irin hanya zai bi da Koriya ta kudu ba kan batun Nukiliyar Koriya ta Arewa, a dai dai lokacinda yake shirin taron koli da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un kafin nan da watan Mayu.


Sai dai Amurka da wakilan Koriyan sun sanar da sabunta yarjejeniya a cikin wannan mako. Yarjejeniyar ta fitar da Koriya ta Kudu daga cikin kasashen da Amurka ta dorawa haraji, yayin da kuma ta rage shigowar karafa daga Koriyaa ta Kudun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG