Jiya Lahadi shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da tunanin da ake yi cewa, ya kasa samun gogaggun lauyoyi da zasu kare shi a binciken katsalandan da Rasha tayi a zaben Amurka, duk da cewar wasu lauyoyi biyu da aka bada sanarwar zasu shiga sahun lauyoyi d a zasu kare shi, yanzu ya fasa daukar su.
Wani tsohon babban lauyan gwamnatin Amurka Joseph Di Genova, da uwargidansa Victoria Toensing, sun amince a makon da ya gabata cewa zasu shiga jerin lauyoyi da zasu kare shugaban na Amurka.
Sa’o’i bayan da Trump ya bayyana farin cikinsa a shafinsa na Tweeter a kan rukunin lauyoyinsa, sai lauyansa Jay Sekulow, ya fada cewa Digenova da matarsa Toesing, basu cikin layuyoyin da zasu kare Trump dangane da zargin hada baki tsakanin kwamitin yakin neman zabensa da kasar Rasha, a zaben shekarar 2016 wai hakan ya taimaka masa ya lashe zaben da kuma zargin yiwa binciken katsalanda da murda gaskiya.
Sabuwar gyarar huska a rukunin lauyoyin Trump na zuwa ne bayan kwanaki da jagoran lauyoyin da suke kare shi kan wannan zargi John Dowd ya janye cikin lauyoyin, yayin da wani shahararren lauya a nan Washington, Theodore Olson yaki amsa gayyatar zama daya daga cikin lauyoyin da suke kare Trump.
Facebook Forum