Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ba Da Umurni Dakatar Da Daukan Masu Sauya Jinsi a Aikin Soja


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umurnin a dakatar da daukar duk wan wanda ya canza jinsin sa aikin soja.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umurnin cewa daga yanzu kar sake daukar duk wani wanda ya canza jinsin sa aikin soja,sai ko idan ya zame babu wani zabi.

Wannan umurnin na kunshe cikin wata sanarwan da fadar White House ta fitar, wadda tace sakataren tsaron cikin gida yanzu haka ya kammala tantance wadanda suke da tarihin canjin jinsin su domin wadannan suna da rauni a gudanar da ayyukan soja har na wani tsawon lokaci.

Tun a cikin shekarar data gabatane shugaba Trump yayi yunkurin dakile masu canjin jinsin daga shiga aikin soja, amma hakan yayi karo da yunkurin nan na shugaba Obama na amincewa dasu.

Trump yayi kokarin ganin wannan ya samu amincewar majilisa amma hakan ya samu kalubale daga harkokin sharar abinda yasa tilas aka fara daukar su acikin watan janairu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG