A jwabin na Mr. Obama, jiya Alhamis, ya jaddada cewa babban abu dake kan ajendarsa shine tabbatar da lafiyar Amurkawa, biyo bayan mummunar harin da aka kai a garin San Bernadino cikin jihar California, da kuma wanda aka kai a birnin Paris, duka hare haren biyu, magoya bayan kungiyar ISIS suka kai su.
Shugaban wanda yayi magana bayan wani taro da dukkan jamai'an majalisar tsaro dake karkashinsa na lokaci mai tsawo, yace yanke hukuncin cewa babu wata barazanar a kawowa kasar harin ta'addancin, ya ta'allaka ne a bangare daya, kan cikakken dukkan matakai a fadin gwamnatin, na hana kai hari da kuma kare kasar.
Da yake magana ga Amurkawa baki daya, daga cibiyar hana hare haren ta'addanci, dake bayan garin birnin Washington DC, Obama yace, "tilas ne mu kara kulawa."