Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kawancen da Amurka Ke Jagoranta Ya Halaka Manyan Shugabannin ISIS


Shugabannin ISIS Uku
Shugabannin ISIS Uku

Ma'aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon, tace farmakin da jiragen sama na yaki da rundunar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci suka kai a Iraqi da Syria sun halaka manyan shugabannin kungiyar ISIS guda uku, ciki harda ma'ajin kungiyar.

Kakakin rundunar taron dangin Steve Warren, ya fada jiya Alhamis cewa, Abu Salah shine yake kula da harkokin murdiya da kwace na ISIS. Warren ya kira Salah daya daga cikin kwararrun shugabannin kungiyar ISIS, saboda haka mutuwarsa zata kassara samun kudadenta.

Hakan nan kakakin yace, hare haren da rundunar taron dangin take kaiwa sun halaka mayakan sakai na ISIS su 350, a birnin Ramadi dake Iraqi. Harma sojojin kasar sun sake kwace wani bangare na birnin makon jiya, amma Daesh tana rike sauran garin.

Hakan nan a jiya Alhamis, wani babban jami'i a Baitulmalin Amurka,Adam Szubin, yace kungiyar ISIS tana da dukiya, wacce kassara hanyoyin samun kudadenta suna da wuya.

Mr. Szubin wanda yake sashen tattara bayanan sirri dangane da ta'addanci da hanyoyin samun kudaden su, yayi magana ce a Ingila inda yace kungiyar tana samun fiyeda dala miliyan 500 daga sumogan mai, da kuma kusan dala miliyan dubu daya wacce ta wawushe daga asusun bankuna a Iraqi da Syria, da kuma wasu miliyoyi data kwace daga hanun wasu 'yan kasashen biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG