Jiya da dare shugaban Amurka Barack Obama ya yiwa kasar jawabi akan kashe kashen da wasu mutane biyu mata da miji suka yi a San Barnerdino dake jihar California inda suka hallaka mutane 14 tare da jikata wasu 21.
Yace abun da ya faru abun bakin ciki ne kuma kasar ba zata zuba ido ta ga ana kashe mata mutane ba. Yace zasu bi digdigin abun da ya faru kuma su dauki matakan da suka dace.
Shugaban yace har yanzu hukumar bincike ta FBI tana cigaba da tara bayanai akan abun da ya faru. Amma kawo yanzu babu wata shaida da ta nuna maharan nada alaka da kungiyoyin ta'adanci a kasashen waje.
Yace Amurka ta karfafa matakan tsaro akan barazanar ta'adanci. Kazalika sojojin Amurka suna bin sawun 'yan ta'ada koina a duniya.
Amma yace ya luira yanzu 'yan ta'ada sun koma yin anfani da hanyoyin da basu da sarkakiya kamar yadda suka yi a California.
Shugaba Obama yace amurkawa sun soma tababan ko zasu iya shawo kan ta'adanci . Amma yace zasu murkushe kungiyar ISIS.
Shugaban ya yi alkawarin cewa sojojin Amurka zasu cigaba da farautar shugabannin 'yan ta'ada a kowace kasa suke samun mafaka. Amurka zata cigaba da dinga ba sojojin Syria da na Iraqi dake fafatawa da kungiyar ISIS horo da kayan aiki. Kazalika Amurka tana aiki kafada da kafada da kawayenta. Bugu da kari kasashen duniya sun soma kokarin kawo karshen yakin Syria.
Kafin ya kammala jawabinsa ya kira 'yan kasar kada su nunawa kowa banbanci. Ya kuma kira kasashen musulmai da su karfafa yaki da mugun akidar 'yan ta'adan dake kiran kansu musulmai.
Ya kira 'yan majalisar kasar da su dauki matakan da zasu hana duk wani dan ta'ada mallakar makamai.
Ita ma ma'aikatar shige da fice ta kasar yace ta sa sake nazari akan ba mutane takardar shigowa kasar musamman wadanda suke fitowa daga kasashen da Amurka bata bukatar su nemi visa.
Ga karin bayani.