White House tace wannan itace ahuwa mafi yawa da aka yiwa ‘yan hursuna a rana guda cikin shekaru da yawa da suka gabata.
Sakin wadannan mutanen dai yana cikin yunkurin Shugaba Obama na ganin an samu gyara ga halayyar mutanen da aka tsare na tsawon lokacin da yake tilas ne a tsare su.
Shugaban yayi haka ne domin ganin an rage tsananin hukuncin da aka yanke wa hursunonin da basu da mummunar laifin tashin hankali dake da nasaba da batun muggan kwayoyi.
Wannan ahuwar dai ya nuna raayin sa cewa akwai bukatar rage yawan hukuncin tsare mutane wanda hakan ya tura dubban Amurkawa zaman gidan yari akan abinda bai kai ya kawo ba.
Wasu daga cikin wadanda wannan ahuwar shugaban kasa ta shafa ko sun hada da mutane 67 da aka daure na tsawon rai da rai.