Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Yiwa Wasu Firsinoni Ahuwa


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Al'ada ce a nan Amurka shugaban kasa ya nunawa firsinoni tausayi ta sakin wasu daga cikinsu

Bayanai da dumi duminsu sun nuna cewa shugaban Amurka Barack Obama ya yiwa wasu firsinoni ahuwa.

Yau shugaban ya shaidawa duniya sakin wasu firsinoni dari biyu da goma sha hudu daga gidajen kaso daban daban na gwamnatin tarayya.

Daya daga cikin gidajen kason Amurka
Daya daga cikin gidajen kason Amurka

Sakin wadannan firsinonin ya zo daidai lokacin da aka fara fafutikar neman zabe na shugabancin kasar da na majalisun tarayya da na jihohi.

Yanzu dai ba'a san irin tasirin da sakin wadannan firsinonin zai yi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG