Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Singapore Zasu Kaddamar Da Yarjejeniyar Yankin Pacific


Shugaban Obama da Farai ministan Singapore
Shugaban Obama da Farai ministan Singapore

Shugaba Obama da Firaministan Singapore Lee Hsien Loong, sun jaddada aniyarsu ta kaddamar da 'yarjajjeniyar yankin Pacific ta Trans-Pacific mai cike da takaddama.

Jiya Talata a Fadar White House, Obama da Lee sun tattauna kan yarjajjeniyar ta kasashen yankin Pacific ko TPP, wadda yarjajjeniyar cinakayya ce ta kasashe 12, wadda ka kasa gaba ko baya.

"Mafitar ba ita ce ficewa daga 'yarjajjeniyar cinakayyar da duniya baki daya ba," a cewar Shugaba Obama jiya Talata. Shi kuwa Lee cewa ya yi, "Mu na fata, kuma na san cewa shi ma Shugaba Obama na wannan fatan, cewa Majalisar Tarayyar za ta amince da TPP kwanan nan," a cewar Lee.

Lee ya kuma ce wannan yarjajjeniyar za ta bai wa Amurka damar ma'amala mai kyau da kasuwannin da ke kunshe da kashi 40% na tattalin arzikin duniya.

XS
SM
MD
LG