Jiya Talata, Kotun kolin China ta ce masuntan da ke shiga ruwayen China fiye da sau daya a shekara za a ci su tara tare kuma da daurin shekara guda a kurkuku. Kotun ta kuma tanaji hukunci kan kama sauran halittun ruwan.
A watan jiya, wata kotun Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Hague ta zartas da hukunci cewa kasar China ba ta da iko kan ruwayen na tekun Kudancin China, ciki har da wani yanki mai kunshe da albarkatu mai tsawon mil 200 da ke tsibirin Spratly.
Ministan Tsaron China Chang Wanquan ya yi gargadin kan yiwuwar barazana ga tsaron China daga gabar teku, inda ya yi gargadin cewa ya kamata China ta kintsa don yiwuwar shiga abin da ya kira "yakin al'umma a Teku" don kare kasar.
Ita ko Japan, da ta ke nazarin yanayin tsaro a yankin a jiya Talata, ta ce China fa ka iya kuskuren takalo wani al'amari mai mummunan sakamako saboda manufofinta masu cike da takala.
Kotun Dindindin ta sasanta rigingimun iyaka, ta zartas da hukunci cewa gine-ginen da China ke yi a yankin, sun yi mummunar illa ga halittu a yankin.