Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Musanta Kai Hari da Iskar Gas a Siriya


 Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha
Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha

Rasha ta musanta ikirarin da ‘yan tawayen Syria da kungiyoyin kare hakkin bil’adama suke yi cewa ita ke da alhakin harin gubar iskar gas da aka kai yau a daidai inda aka harbor jirgin Rasha mai saukar angulu a lokutan baya, bisa ga cewar kafofin sadarwar kasar Rasha.

Wani ma’aikacin jinkai a arewa maso gabashin Syria da yaki ya daidaita yace wani jirgi mai saukar angulu ya sako garewannin iskar gas mai guba a ganin kusa da birnin Aleppo da aka mamaye.

A kalla mutane talatin galibi mata da kananan yara ne iskar gas din ta yiwa illa, da ma’aikatan suka ce An zubo da dare kusa da inda ‘yan tawaye suka kakkabo wani jirgin Rasha mai saukar angulu. Kawo yanzu ba a san irin illar da gubar tayi ba.

Jirgin Rasha mai saukar angulu da aka rikto a Siriya
Jirgin Rasha mai saukar angulu da aka rikto a Siriya

I zuwa jiya Talata da yamma, akwai rahotannin dake karo da juna a kan wanda ya kai harin. ‘yan tawayen dake kokarin kwato birnin Aleppo da aka mamaye da kuma dakarun gwamnati da suka yiwa birnin kawanya suna tsirawa juna hannu da amfani da iskar gas mai guba.

Kawo yanzu gwamnatin Syria dake yakin kwace ikon yankin da ‘yan tawaye bata ce komi ba game da lamarin da masu kula da lamura suka bayyana a matsayin fada mafi muni a cikin watanni da dama.

XS
SM
MD
LG