Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Republican Na Kara Kushewwa Dan Takararsu Donald Trump


Dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump
Dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump

Daukar mako guda da Donald Trump ya yi yana jayayya da Khizr da Ghazala Khan, wadansu Musulmi iyayen wani soja da aka kashe a Iraq, ya sa karin ‘yan jam’iyar Republican fitowa fili suna caccakar dan takarar, wani abinda ke kara nuna irin rashin jituwar dake tsakanin kusoshin jam’iyar.

Meg Whitman, wata fitacciyar jami’ar fasaha, da ta nemi kujerar gwamnan California amma bata samu ba a shekarar dubu da dari biyu da goma ta shaidawa jaridar New York Times jiya Talata cewa,zata goyi baya ta kuma jagoranci nemarwa ‘yar takarar jam’iyar Democrat Hillary Clinton tallafin kudin yakin neman zabe, tare da bayyana Trump a matsayin marar gaskiya.

Khizr Khan,musulmi, wanda ya rasa dansa a Iraqi da Trump ya cacaka
Khizr Khan,musulmi, wanda ya rasa dansa a Iraqi da Trump ya cacaka

Dan majalisar dattijai daga jihar New York Richard Hanna ya zama dan jam’iyar Republican na farko da ya nuna goyon bayan Clinton inda yace hankalinsa ya tashi da jin kalaman dan takarar jam’iyar Republican din a kan iyalin Khan.

Wadannan goyon bayan sunzo ne ‘yan sa’oi bayanda shugaban Amurka Barak Obama ya dauki matakin ba sabanba, inda shugaban kasa mai ci, ya kwabi dan takarar shugaban kasa, inda ya bayyana Trump a matsayin wanda bai cancanci zama shugaban kasa ba

Trump baiyi wata wata ba, ya maida martani ta hanyar twitter inda ya bayyana cewa, Shugaba Obama ya karrama shi da ambatonsa da ya yi, ya kuma kara da cewa, Obama bai san abinda yake yi ba, tare da bayyana shi a matsayin shugaban jeka na yika.

An fara wannan takaddamar ce bayanda Khizr Khan , mahaifin wani sojan Amurka da aka kashe a bakin daga ya kushewa shirin Trump dan takarar jam’iyar Republican na hana Musulmi ‘yan kasashen ketare shiga Amurka. Khan yace da an yi haka da danshi bai shiga aikin soja a Amurka ba. Trump ya maida martani da cewa, mahaifiyar sojan bata yi magana ba, domin bata da ‘yancin magana.

XS
SM
MD
LG