Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Ya Kasa Zuwa Chibok


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Bayan wata daya da sace daliban makarantar 'yan mata dake Chibok a kudancin jihar Borno har yanzu shugaban kasar ya kasa ziyarar garin

Biyo bayan ta'asar da aka yi a makarantar 'yan mata dake Chibok inda aka sace dalibai kusan dari uku masu kula da harkokin yau da kullum sun sa ido su ga ko shugaban kasa zai ziyarci garin.

A daidai lokacin da jami'an tsaro na wasu kasashen duniya ke isowa Najeriya domin su taimakawa kasar kubuto daliban da kungiyar Boko Haram ta sace, 'yan kasa na nuna damuwarsu da yadda shugaba Jonathan ya kasa kai ziyarar gani da ido da jajantawa iyaye da al'ummar yankin da lamarin ya faru.

Wani mai fashin baki Malam Shuaibu Mungadi yace babu mamaki idan shugaba Jonathan ya nuna sha'awar kai ziyara garin Chibok kuma babu mamaki idan yayi biris. Yace amma idan yayi biris aikin masu bashi shawara ne su jawo hankalinsa. Da daya daga cikin masu bashi shawara daga yankin da ake yawan fitinu ya fito,wato Ahmed Gulak. Shi ya kamata ya fadakar da shugaban kasa yayi abun da ya dace. Amma abun mamaki ranar da aka kashe wasu dalibai a Yobe ranar shugaban ya tafi wani biki a Kano. Haka ma kwana daya bayan an tayar da bamabamai a Nyanya sai ga shugaban kasa a Kano wurin gangamin siyasa har da raye-raye. Wannan ya kara nuna halin "ko oho" dashi da masu bashi shawara su keyi.

Malam Mungadi yace bai dace ba a koina a duniya a ce an jefa yara kusan dari uku da iyayensu cikin wani mawuyacin hali sabili da rikicin dake faruwa a kasar kana a ce shugaban kasa bai ji a jikinsa ba ko ma ya ziyarci yankin da abun ya shafa. Maimakon yin juyayi ma sai shugaban kasa ya cigaba da taron tattalin arzikin duniya. Idan da masu bashi shawara suna aikata gaskiya da sun bashi shawara ya daga taron har zuwa wani lokaci.

Saidai kuma hankalin mahalarta taron kacokan ya koma kan daliban da aka sace da kuma matasalar tsaro a kasar gaba daya.

Daya daga cikin shugabannin jam'iyyar PDP Barrrister Abdullahi Jalo cewa yakamata 'yan Najeriya su fahimci lallurar da kasar ke ciki kuma kada a nuna cewa gwamnati bata kula da abubuwan dake faruwa ba. Yace da lamarin ya faru shugaban kasa ya soke tafiya taron jam'iyyarsu da suka shirya zasu yi a Yola jihar Adamawa. Yace ba zuwa yin jaje yake da mahimmanci ba illa a samo yaran da ransu. Wannan shi ne abun da shugaban kasa ya sa a gabansa.

Ga rahoton Umar Faruk
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:27 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG