Yau wata guda ke nan da 'yan ta'adan kungiyar Boko Haram suka sace daliban makarantar 'yan mata dake garin Chibok cikin jihar Borno. Sace daliban ya jawo takaddama da nuna yatsa tsakanin jihar Borno da gwamnatin tarayya. Wasu masu zaman kansu da kungiyoyi suma sun shiga yin cecekuce akan wannan bala'in da aka yi a Chibok.
Alamura da dama sun biyo bayan sace daliban kama daga kokwanton da shugabar matan PDP tayi inda ta kawo shakka akan sace yaran da yadda matar shugaban kasa ta ci zarafin jami'an gwamnatin jihar ta Borno. Wasu kasashen duniya ba ba'a barsu baya ba domin sun shiga zanga-zanga suna yin tur da lamarin suna kuma bukatar da a sako yaran cikin gaggawa.
Duk da nuna yatsar da gwamnatin tarayya keyi, gwamnatin Borno ta daurawa gwamnatin tarayya alhakin abun da ya faru. Da yake magana gwamnan jihar Ibrahim Shettima yace daren da za'a kai hari a Chibok wasu kauyawa dake kusa da garin sun shaidawa shugaban karamar hukumar Chibok wanda nan take ya shaidawa DPO na 'yan sanda da kwamandan sojoji dake garin. Duk wadannan sun tabbatarwa shugaban karamar hukumar cewa sun shirya masu.
Kalamun Gwamna Shettima sun zo daya dana kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, wadda a baya-bayannan tace hukumomin Najeriya sun san za'a kai hari Chibok, amma suka kawar da kai. Sojojin Najeriya sun musanta.
Gwamnan ya cigaba da cewa akwai wasu abu da ba zai fada ba yanzu. Idan lokaci yayi zai yi magana domin kura-kurai biyu basu kawo gyara. Yace ba batun sadakarda mulki ba kawai har ma da rayuwarsa ashirye yake ya sadakarda ita idan za'a samu zaman lafiya a kasar.
Dangane da matar shugaban kasa gwamna Shettima yace babu wani bangaren tsarin mulkin kasa da ya baiwa matar shugaban kasa yin abun da ta yi. Yace bata da izinin cin mutuncin mutane. Yace ba zasu amince da wani yana zaune a Aso Rock yana cin mutuncin mutane ba.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.