Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Dake Bidiyon Shekau Daliban Chibok Ne


Hoto daga bidiyon da Abubakar Shekau ya fitar yana neman ayi musayar daliban Cibok da mayakansa dake hannun hukumomin Najeriya.
Hoto daga bidiyon da Abubakar Shekau ya fitar yana neman ayi musayar daliban Cibok da mayakansa dake hannun hukumomin Najeriya.

Daya daga cikin iyayen daliban Chibok ta tabbatar cewa ta ga 'yarta a cikin jerin yaran dake cikin hotunan bidiyon da mutumin dake cewa shine shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar a baya-bayannan.

Wannan mahaifiya da muka sakaye sunanta saboda tsaro ta nuna damuwarta ganin tabbacin cewa 'yarta na hannun 'yan bindigan nan wadanda suka dauki alhakin kashe dubban mutane a shekarun baya, musamman a arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan bidiyo an yada shi ne akan yanar gizo, inda Mr. Shekau ya nemi ayi musayar daliban yara, da mayakanshi dake hannun hukumomin Najeriya.

Jaridar Rueters itama ta bada rahoton dake cewa wata uwa ta gane fuskar 'yarta a cikin bidiyon da Shekau ya fitar, kuma ta nuna damuwarta da lamarin, tana mai samun karfin gwiwar ganin agajin kasa da kasa, amma tayi korafin rashin ganin jami'an tsaron Najeriya.

Matan dai kiyasin su zai kai 130, ba'a da tabbacin inda ragowarsu suke, da kuma lokacin da aka dauki wannan hoto, da kuma inda suke a lokacin da aka dauki hotunan bidiyon.

Matsalolin tsaro a arewacin Najeriya sunyi tsami, da har ta kaiga kungiyoyin kasa da kasa da shuwagabannin duniya suna kai dauki kusan bai daya.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG