Kasa da sa'o'i ashirin da hudu da sojojin Amurka suka isa Najeriya domin taimakawa wasu daga arewa maso gabashin kasar sun soma tofa albarkacin bakinsu.
Wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu ta zanta da Malam Zakari Adamu na rundunar adalci dake jihar Yobe da Malam Danladi Lawal wani mazaunin garin Potiskum. Dukansu sun ce shugaba Jonathan yayi amai amma ya lashe sabili da haka suna rokonsa ya sauka daga mukaminsa.
Zakari Adamu yace lamarin da ya faru ya tayarwa duk wani dan Najeriya hankali musamman al'ummar arewa maso gabas. Sace yaran da 'yan Boko Haram suka yi ya sa duniya gaba dayanta abun da take magana ke nan akai yanzu. Yace abun takaici kuma abun bakin ciki shi ne a ce an shiga makaranta an sace yara kusan dari uku kuma kasar ta kasa yin komi duk da sojoji da kayan yaki da ake ikirarin kasar nada su. Abun kunya ne a ce wai sai kasashen waje sun zo sun taimakawa kasar.
Akwai kasashen da an yi abun kunyan da bai kai na Najeriya ba amma shugabanninsu suka yi murabus. Sabili da wanna lamarin kamata yayi shugaban kasa yayi murabus. Ya sauka ya fadawa duniya ya kasa. A bar mai iyawa ya karbi mulki.
Malam Danladi Lawal yace a ce an sace mutane kusan dari uku an kuma kashe wasu dari uku duk sun nuna kasar bata da shugabancin kwarai. A halin da ake ciki babu anfanin gwamnati domin haka a sake wani.
Kawo yanzu dai jami'an Amurka sun isa Najeriya kuma tuni sun fara aiki.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.