Kalamun Bamanga Tukur tamkar sa takalmin karfe ne inda ya yi barazanar take duk wani mai muamala da wadanda suke karkashin shugabancin Kawu Baraje da shi Baranjen ma kansa. Kalamun nasa sun fito da zafi kuma alamu ne na cewa babu sulhu nan kusa.
Zaben da jam'iyyar ta yi ranar Asabar da ta gabata tamkar bata sauya zani ba domin mukaraban Bamanga Tukur suka sake dawowa a zaben cike gurbin. To sai dai yayin da Bamanga Tukur ya dauki matakin rusa sulhu ana raderadin cewa takardar shaidar rajista ta jam'iyyar tana hannun bangaren Kawu Baraje.
Mataimakin Bamanga Tukur Sanato Abubakar Gada ya ce duk wanda yake rike da mallakar PDP kuma ba jam'iyya ce ta zabeshi ba to ya karya doka. A kan batun cewa wadanda suka balle na iya shiga jam'iyyar adawa sai ya ce kowa na da 'yancin ya shiga kowace jam'iyya. Ya kara da cewa ba dole bane su zauna cikin jam'iyyar PDP.
Sanato Hadi Sirika na jam'iyyar APC ya ce abun da Bamanga Tukur ya fada ya saba ma doka. Ma'ana ba zai iya cire wadanda aka zaba ba daga mukamansu. Ya ce su da suke adawa da yanzu su ne masu rinjaye.
Alamu na nuna cewa 'yan sabuwar jam'iyyar PDP ba zasu rawarawa ba da barazanar Bamanga Tukur ta barin mukamansu ko su nemi gafara daga bangarensa.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.