Matakin ya shafi kusan ma'aurata rabin miliyan Amurkawa da yara 50,000 wadanda ba 'yan asalin kasar ba wadanda iyayensu su ka auri Ba’amurke.
Da yake sanar da shirin, Shugaba Biden ya ce,"Sun shafe a kalla shekaru goma suna zaune a nan Amurka. Wadannan ma'auratan suna renon iyalai, suna tura 'ya'yansu Coci da makaranta, suna biyan haraji, suna ba da gudummawa ga kasarmu na tsawon shekaru goma ko fiye. A gaskiya ma, tsawon shekarun da mutanen da abin ya shafa suka shafe a nan shine shekaru 23, amma suna zaune a Amurka duk wannan lokacin, cikin tsoro da rashin tabbas za mu iya gyara wannan yau, kuma abinda mu ke yi ke nan."
Kafin dan gudun hijira ya iya cin moriyar sabon tsarin, tilas ne ya zauna a Amurka na tsawon shekaru 10 ko fiye, kuma ya kasance yana auren Ba’amurke bisa dokar kasa, a ranar 17 ga watan Yuni, 2024, bisa ga cewar wata takardar bayanai ta fadar White House.
Har ila yau, a cikin sanarwar ta Shugaba Biden, akwai shirin samar da bizar aiki ga wadanda su ke cikin rukunin yaran da iyayensu bakin haure, su ka shiga kasar su ka sa su makaranta da ake kira DACA, wadanda ke da takardar shaidar samun digiri na Amurka da kuma tayin aikin yi da ya shafi kwarewar su.
Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wata guda da Shugaba Biden ya dauki matakin zartaswa kan shige da fice - kuma a bisa doka. A farkon watan Yuni, ya yi amfani da ikon shugaban kasa da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya sha amfani da shi wajen hana mafaka ga galibin bakin haure da ke bi ta kan iyakar Amurka da Mexico su ka shiga Amurka.
Dandalin Mu Tattauna