Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Dauki Tsatsauran Matakin Hana Bakin Haure Shiga Amurka Ta Iyakar Mexico


Shugaban Amurka Joe Biden, Washington Yuni 04, 2024.
Shugaban Amurka Joe Biden, Washington Yuni 04, 2024.

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya hannu a wasu tsauraran matakan hana karban ‘yan ci rani masu neman mafaka da suke shiga Amurka ta iyakar kasar da Mexico ba bisa ka’ida ba, a wani babban mataki yayin da zaben shugaban kasa na watan Nuwamba ke karatowa.

WASHINGTON, D. C. - ‘Yan ci rani da aka kama suna ketara iyakar ba bisa ka'ida ba, za a tasa keyarsu cikin sauri ko kuma a mayar da su Mexico a karkashin wannan mataki.

Sai dai wannan matakin ba zai shafi yara kanana da basu tare da wani babba ba, da kuma mutanen da suke fuskantar tsananin rashin lafiya ko babbar barazana, da kuma waɗanda aka yi fataucin su, in ji Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka.

Biden, ‘dan jam'iyyar Democrat, ya tsaurara matakan tsaro a kan iyakar, yayin da shigowar bakin haure ya kasance wani babban lamari ga Amurkawa a zaben da za a yi a ranar 5 ga watan Nuwamba, inda zai fafata da tsohon shugaban kasar Donald Trump na jam’iyyar Republican, wanda ya dauki tsauraran matakai a game da shige da fice a gwamnatinsa, kuma ya sha alwashin zage damtse idan aka sake zabensa.

Biden ya hau karagar mulki a shekarar 2021 yana mai alwashin sauya wasu tsare-tsare na hana shige da fice da Trump ya bullo da su. Sai dai gwamnatinsa ta fuskanci kalubale na samun kwararowar bakin haure mafiya yawa, wani abu da yake neman fin karfin hukumomin kula da iyakokin Amurka, sannan birane suke ta samun sabbin masu isowa.

A yayin wani taron manema labarai na Fadar White House, Biden ya ce damar samun mafaka za ta kasance ga bakin hauren da suka yi rajista ta wata manhaja, CBP One ko kuma suka yi amfani da wasu hanyoyin bin doka maimakon ketara iyaka ba bisa ƙa'ida ba

"Wannan matakin zai taimaka mana wajen samun iko kan iyakokinmu da kuma dawo da tsari," in ji Biden. "Wannan dokar za ta ci gaba da kasancewa har sai a rage yawan mutanen da ke kokarin shigowa ba bisa ka'ida ba zuwa matakin da tsarinmu zai iya karbar su yadda ya kamata."

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG