Wannan wani mataki ne da ya shafi batun shigowa kasar a shekarar zabe, da tuni da dama da ga cikin yan Democrat su ka nema.
Biden ya marabci wani buki a fadar white house, na wani shirin da aka assasa a zamanin Obama da ya bayar da kariya ga iza keyar matasan da suka shugo kasar da ba’a dauki bayanan su ba zuwa kasashen su, zai kuma sanar da sabon shirin a lokacin, kamar yadda wadansu mutane uku da fadar white house ta yiwa bayani ga me da shirin su ka bayyana.
Biyu da ga cikin mutanen da aka yi wa bayanin, sun bayyana cewa, tsarin zai bada dama ga kusan ma’aurata 490,000 su mika takardun neman mafaka a karkashin shirin, wanda zai kange su daga iza keyar su zuwa kasashen su, da ba su iznin yin aiki, idan har sun kai shekaru a kalla 10 a cikin kasar.
Duk mutanen dai sun yi magana ne bayan da suka nemi a saya sunayen su, saboda ba a basu damar tattauna batun a bainar jama’a ba.
Fadar white house ta ki cewa uffan akan sanarwar, lokacin da aka nemi ta yi hakan a jiya Litinin.
Dandalin Mu Tattauna