Morocco da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, na shirin karawa a gasar cin kofn duniya a zagayen kusa da na karshe.
Wanda ya lashe wannan wasa zai hadu da Argentina wacce ta doke Croatia da ci 3-0 a zagayen kusa da na karshe a ranar Talata.
Magoya bayan kasashen biyu suna ta shirye-shiryen kallon wannan karawa, kama daga Paris babban birnin Faransa zuwa Rabbat, babban birnin Morocco.
“Komai zai iya faruwa a wasan, nasarar Morocco ce za ta ba da mamaki, amma nasara ga Faransa, wani abu ne da duk duniya sharhi da hasashe suka fi karfi a kai.” In ji Abdulkarim A. Tsoho, mai sharhi kan kallon kwafa.
Faransa ta yi wa Morocco mulkin mallaka tsakanin 1912-1952, lamarin da ake ganin zai yi tasiri a wannan karawar da za a yi.
Tsoho ya kara da cewa, akwai mutane da dama da ke nuni da cewa, da ma kasashen Afirka na da kwarewar da za su iya kai wa wannan mataki amma akan danne su ta wasu hanyoyin dabarun taka leda.
Wannan shi ne karon farko da wata kasa daga nahiyar Afirka da yankin kasashen larabawa, ta samu damar zuwa zagayen kusa da na karshe a gasar kofin duniya.
Faransa ita ke rike da kofin gasar, kuma mafi akasarin hasashen da masana ke yi na nuni da cewa, ita aka fi tsammanin za ta yi zarra a wasan.
Ko da yake, duba da irin nasarori na ba-zata da suka faru a wannan gasa, a daya gefen, wasu na ganin komai na iya faruwa.