Yayin ziyarar gani da ido jami'ar hukumar a Najeriya Mrs Angela Dekongo Atenga tace akwai bukatar a mutunta wadanda Kamaru ke tasa keyarsu zuwa Najeriya.
Jami'ar tace tuni hukumar ta aikewa hukumomin Kamaru korafi domin daukan mataki. Tashe wakilinsu na Kamaru ya rubutawa gwamnatin Kamaru akan lamarin. Akwai bukatar a mutunta masu gudun hijira koina suke.
Kodayake kasar Kamarun ta karbi 'yan gudun hijiran wasunsu sun ki zuwa inda gwamnatin ta tanada masu saboda wurin ya yi kusa da iyaka da Najeriya kuma 'yan Boko Haram na kutsawa su shiga sansanin.
Dama hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya ta dade tana korafi akan yadda Kamaru ke wulakanta 'yan gudun hijiran.
Sa'adu Bello na hukumar bada gajin gaggawa ta Najeriya dake kula da yankin Adamawa yace dole ne a dauki mataki. Yace alatilas gwamnatin Kamaru ta tasa keyar 'yan gudun hijiran zuwa Najeriya ba tare da la'akari da halin tsaronsu ba ko ci da shansu.
Ita dai Kamaru ana zargeta da yiwa 'yan gudun hijiran korar kare ne.
Ga karin bayani.