An yi wani taro na sulhu tsakanin shugaba Muhammadu Buhari, da shugabanin majalisar kasa domin warware duk wata takaddama ko rashin fahimtan dake tsakanin bangarorin biyu.
Bisa ga kiran da majalisar wakilan ta Najeriya tayi a kwananan cewa ya kamata a shiga tsakani domin a sulhunta bagarorin biyu domin kada alamuran demokradiya su ci gaba da durkushewa a kasar.
Koda yake ba’a bada wata sanarwa takamammiya dangane da wannan taron ba shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya bayanawa manema labaru cewa taron da aka saba yi tsakanin bangarorin Gwamnatin biyu.
Ba’a kira wannan taron domin tattauna wani abunda aka fara harsashe ba ko maganar Ministoci ko kuma wata takaddama da akayi hasashe ba.
Wani kwararre aka sha’anin majalisa Farfesa al-Mustapha Osuji, ya ce wannan ganawa da bangarorin biyu suka yi yana da mahimmaci domin zai taimaka wajen habaka demokradiya a Najeriya, da kuma baiwa kowane bangare yancin sa ,domin shi shugaban majalisar dattawa shine shugaban majalisa baki dayan ta a tsarin zaman majalisa kuma idan aka ce basu ganawa da shugaban kasa abun na iya kawo cikas.