Wadanda lamarin ya shafa sun hada da shugabannin kananan hukumomin Gumel da Jahun da Birnuiwa.
Majalisar ta zargi shugabannin uku da karya dokoki da ka'idodjin kashe kudaden gwamnati.
Onarebul Sule Musa Dutse mataimakin shugban kwamitin da majalisar ta kafa domin bincika yadda kananan hukumomin jihar ke sarafa kudaden gwamnati yace bincikensu ya nuna cewa yadda aka kashe kudi a kananan hukumomin ba haka doka ta tanada ba.
Matsayinsu shi ne kowace karamar hukuma sai ta bayar da rahoton yadda take kashe kudi kowane kwata. A cikin kananan hukumomi 17, 10 ne kawai suka bada rahoton yadda suka kashe kudi.
To saidai jam'iyyar PDP dake zama uwa ga duk kananan hukumomin tace matakin da majalisa ta dauka ya keta doka.
Alhaji Salisu Mahmuda shugaban jam'iyyar na Jigawa yace siyasa ce. Yace kowane su ukun da aka tsige yana da wata ja da wani jami'in gwamnatin jihar. Misali shugaban karamar hukumar Jahun akwai takunsaka tsakaninsa da kakakin majalisar dokokin jihar.
Jam'iyyar PDP ta sha alwashin zuwa kotu akan lamarin. Shi ma Ambassador Ibrahim Kazaure mataimakin shugaban PDP na kasa mai kula da shiyar arewa maso yammacin Najeriya ya tabbatar da zuwa kotun.
Ga karin bayani.