Kwamishanan labarun hukumar alhazan Najeriya Dr. Saleh Okenwa ya yi bayanin da ya bada adadin mutane 99 da aka tabbatar sun rasu.
Ana cigaba da binciken gano sauran mutane 224 'yan Najeriya da suka bace. Ba'a sani ba ko suna raye ko kuma sun mutu. Ba za'a ce sun mutu ba domin ba'a ga gawarwakinsu ba har yanzu.
Alhaji Kabiru Mubi shi ne shugaban alhazan jihar Adamawa da su ma suka rasa wasu alhazai. Sun samu gawarwakin mutane biyu amma har yanzu basu san inda tara suke ba.
Jihar Bauchi na cikin jihohin da alhazansu suka rasu. Sakataren alhazan jihar Aliyu Suleiman ya yi bayani. A Bauchi an tabbatar da mutuwar mutane uku kana har yanzu suna neman mutane biyu.
Jihar Sokoto ce ta fi hasarar alhazai kodayek ba'a bayyana adadinsu ba.
Har yanzu a can Saudiya akwai 'yan Najeriya bakwai dake asibiti suna jinya.
Ga karin bayani.