Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Yarjejeniyar Fara Dawo Da ‘Yan Gudun Hijirar Najeriya Gida Daga Ketare


'Yan gudun Hijira
'Yan gudun Hijira

Yarjejeniyar dawo da ‘yan gudun hijirar Najeriya kimannin Dubu 80 na nuna yawan ‘yan Najeriya da suka tsallaka ketare, domin tsira da ransu sakamakon futunar Boko Haram.

Kamar yadda shugaban hukumar agajin gaggawa ta Najeriya Sani Cidi, ya bayyana a ganawarsa da tawagar kula da agajin gaggawa da jin kai ta Afirka AU, yace ta hanyar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya aka cimma wannan yarjejeniyar dawo da ‘yan gudun hijirar.

Don yiwuwar mayar da su garuruwansu na asali da hadin gwiwar gwamnatocin jihohinsu da suka fito, musamman ma Borno da Yobe da Adamawa.

Sani Cidi bai fadi lokacin da za a fara kwaso mutanen ba, sai dai yace za a tabbatar an ‘dauko su bisa ra’ayin kansu da kuma mutunta bukatunsu da samar da inda za a tsugunnar dasu bisa ma’ana, koma a samu a mayar da su muhallansu na asali.

Komishiniyar hukumar agajin gaggawa da jin ‘kai ta kungiyar Afirka Aisha Laraba Abdullahi, tace alkalumansu sun nuna akwai wadanda suka rasa matsugunnansu wanda suke zaune a sansanoni a Najeriya su Miliyan 13, haka nan akwai ‘yan Najeriya Miliyan 3 da sukayi gudun hijira zuwa ketare.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG