Kwamandan hukumar Ibrahim Abdullahi ya gurfanar da mutanen guda hudu a gaban manema labarai, wadanda suke sayar da naman mushe, naman dabbobin da ba'a san cutar da ta kashesu ba wanda kuma baya cikin halal.
Kwamandan yace nan ba da jimawa ba za'a gurfanar dasu a gaban kotu domin a yi masu shari'ar da ta dace dasu. Mutanen dai basu da alaka da saya ko sayar da dabbobi.
Ibrahim Abdullahi ya ja kunnuwan mazauna garin dangane da mutanen da ya kira 'yan bola jari domin su ne suke bi suna zakulo dabbobin da suka mutu, su gyarasu kana su sayarwa jama'a. Sukan yi suya da wasu wasu kuma su sayar a matsayin danyen nama.
Kwamandan yace sun samesu suna gyara dabbobin, jama'a kuma sun ja layi, su saya domin suna ganin sun samu garabasa ne saboda azumi. Suna gap da gyarawa aka cafkesu.
Mutanen da aka kama ba sa azumi saboda wai sun san aikin da suke yi na haram ne. Wani cikinsu da aka zanta dashi yace daga bola suke samo matattun dabbobin.
Ga karin bayani.