Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidauniyar Dangote Ta Soma Rabawa 'Yan Gudun Hijira Tallafi A Jihar Borno


Alhaji Aliko Dangote.
Alhaji Aliko Dangote.

A jihar Borno, Gidauniyar Dangote ta soma rabawa 'yan gudun hijira, wadanda da rikicin Boko Haram ya daidaita, tallafin kayan abinci tare da akawarin bada zunzurutun kudi nera biliyan biyu.

Gidauniyar ta soma rabon kayan abinci ga masu azumi da kuma wadanda suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno.

Gidauniyar tace zata raba kayan abinci ne kyauta ga mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita da yanzu suke samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijira.

Kayan abincin sun hada da sukari da shinkafa da taliya da indomi da man girki da maggi da gishiri da dai sauaran kayan da ake anfani dasu yau da kullum.

Ko a makon jiya gidauniyar ta yi alkawarin bada taimakon nera biliyan biyu ga al'ummar da rikicin Boko Haram ya daidaita a jihar. Amma gwamnan jihar yace zasu mika bukatunsu ga gidauniyar.

Gwamnan ya soma da yabawa gidauniyar dangane da tallafi da take ba al'ummar jihar, musamman a wanan lokacin da suke bukatar irin taimakon da gidauniyar ke bayarwa.

Gwamnan yace idan Allah Ya yadda taimakon nera biliyan biyu da gidauniyar tayi alkawarin bayarwa za'a yi anfani dashi ta hanyar da ta dace. Za'a yi anfani dashi a harkokin kiwon lafiya, ilimi da kuma tallafawa mata.

Gwamna Shettima yace idan sun mika bukatunsu ga gidauniyar, jihar bata son ko sisin kwabo, kuma baya son a aiko da kudin ta hannun gwamnatin jihar Borno. Su yi anfani da kudin su yiwa al'ummar ayyukan da suka dace.

Malama Zuwaira Yusufu itace ta wakilci shugaban gidauniyar wadda ta mika kayan ga gwamnatin jihar Borno. Tace yanzu sun kawo kaya cikin tireloli dari da shida. Kowane iyali zai samu buhun shinkafa, gero, masara da taliya baicin sauran wasu kayan. Taimakon da suka raba baya cikin nera biliyan biyu da suka yi alkawarin basuwa.

Mutanen da aka mika masu tallafin sun bayyana jin dadinsu tare da lissafi abubuwan da suka samu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG