Najeriya ta bukaci a saki hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum sannan kuma gwamnatin mulkin sojan kasar ta ba shi damar zuwa wata kasa, in ji ministan harkokin wajen Najeriya.
A halin yanzu dai Najeriya ce ke shugabantar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka da ake kira ECOWAS, wacce ta kakaba wa Nijar takunkumi bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yuli.
Kungiyar ECOWAS dai ta yi ta kiran a maida Bazoum kan karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, amma gwamnatin sojan kasar ta ci gaba da tsare shi ta kuma ce tana bukatar shekaru har zuwa uku kafin ta maida mulki ga farar hula.
"Muna bukatar su saki shugaba Bazoum domin a ba shi dama ya bar Nijar," abinda ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya fada wa gidan talabijin din Channels kenan a wata hira da aka wallafa a shafin yanar gizo a karshen mako.
"Ba za a ci gaba da tsare shi ba. Zai je wata kasa da ta amince ta karbe shi. Daga nan za mu fara magana kan cire takunkumin da aka sanya wa kasar," a cewar Tuggar.
Ya kuma ce har yanzu kungiyar ECOWAS na a shirye ta tattauna da gwamnatin sojan Nijar.
A ranar 10 ga watan Disamba ne shugabannin kungiyar ECOWAS za su gana a Abuja babban birnin Najeriya domin tattaunawa kan yankin, wanda tun a shekara ta 2020 aka yi ta samun juyin mulkin da ya dora sojoji kan karagar mulki a kasashen Mali, Burkina Faso, Guinea da Nijar.
A watan da ya gabata, wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar Saliyo, ya yi sanadin mutuwar mutane 21, ita ma Saliyo mambar kungiyar ECOWAS ce a cewar manyan jami'an kasar.
Shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, kasar da ita ma mambar ECOWAS ce, ya ce tashin hankalin da aka yi a ranar Asabar wanda ya hada da dogarawan tsaron kasarsa, yunkurin juyin mulki ne.
Dandalin Mu Tattauna