Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Wata Kotun A Landan Ta  Bada Umarnin Kwace Kudaden  Ibori


James Ibori
James Ibori

Jiya Alhamis wani mai shigar da kara a wata kotu Landan ya roki  kotu ta  kwace sama da fam miliyan 100 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 129 daga hannun ‘dan siyasar Najeriya James Ibori, wanda aka samu da laifin damfara, wanda ya kwashe shekaru a gidan yari a Biritaniya.

WASHINGTON, D.C. - A shekarar 2011 ne aka tasa keyar Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur daga birnin Dubai zuwa Landan, inda aka tuhume shi da laifin karkatar da dukiyar da ya tara.

A kuma shekarar 2012 ne ya amsa laifuka 10 da suka hada da zamba da kuma karkatar da kudade, sannan kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari, wani mataki da Birtaniyya ta bayyana a matsayin abin tarihi a yaki da cin hanci da rashawa.

Da alama ana dab da kamala wannan shari’a bayan fiye da shekaru goma ana ta kiki-kaka a kotu da kuma jinkirin kotu, a yunkurin da masu gabatar da kara suka yi na kwace wasu kudade da ake ganin Ibori ya samu ba ta haramtacciyar hanya.

Alkali David Tomlinson na Kotun Southwark Crown ya yi bincike na gaskiya game da kudaden. A zaman da aka yi a jiya Alhamis, bangarorin biyu sun yi muhawara kan yadda za a kidaya adadin da aka kwace, da kuma la’akari da sakamakon da alkali ya yi. Ana sa ran zai kammala kuma ya bayar da umarninsa a hukumance a yau Juma'a ko kuma jim kadan bayan haka.

Lauyan mai shigar da kara Jonathan Kinnear ya shaida wa kotun cewa adadin kudaden da ya kamata a kwace daga hannun Ibori ya kai fam miliyan 101.5, kuma idan bai biya ba sai a yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar zuwa 10 a gidan yari.

Bayan da ya cika rabin hukuncin daurin da aka yanke masa a gidan yari da kuma a tsare bayan shari’a kamar yadda aka saba, Ibori ya koma Najeriya a shekarar 2017 kuma bai halarci zaman na ranar Alhamis ba. Ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters ta hanyar sakon kai ta kwana cewa, yana shirin daukaka kara kan umarnin kwace dukiyar sa.

Ibori har yanzu ya ci gaba da yin tasiri sosai a siyasar Najeriya. Shugaba Bola Tinubu, wanda aka rantsar a watan Mayu, ya karbi bakuncin Ibori sau biyu a fadar shugaban kasa, tare da wasu tsaffin gwamnoni.

Birtaniya ta yi alkawarin mayar da duk wani kudi da aka kwato daga Ibori zuwa Najeriya. A shekarar 2021, ta mayar da Fam miliyan 4.2 da aka kwace daga hannun tsohuwar matar Ibori da kuma ‘yar uwar sa, wadanda su ma suka yi zaman gidan yari saboda sun taimaka masa wajen karkatar da kudade.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG