Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tasa Keyar Wadansu Matasa Biyu Zuwa Amurka Bisa Laifin Razana Mutane Su Biya Toshiya


Samuel Ogoshi, Samson Ogoshi, Ezekiel Ejehem Robert
Samuel Ogoshi, Samson Ogoshi, Ezekiel Ejehem Robert

Masu shigar da kara a Amurka sun sanar da cewa, an tasa keyar wadansu matasa ‘yan Najeriya biyu daga cikin uku da Hukumar FBI ke nema zuwa Amurka, wadanda ake tuhuma da laifin razana matasa samari da ‘yanmata a Michigan da kuma wadansu sassan Amurka don biyan toshiya ko su kunyata su.

Hukumomi a Amurka, sun bayyana cewa, sun yi nasarar kama biyu daga cikin mutane uku da ake tuhuma da laifin hada baki da kuma tilasta mutane, galibi samari da ‘yammata, biyan toshiya bayan sun yaudare su, suka tura masu hotunan batsa.

Jim kadan bayan isowar su Amurka, wani alkali a Amurka Mark Totten ya sanar da cewa, za a gurfanar da Samuel Ogoshi dan shekaru 22, da kanin shi Samson Ogoshi dan shekaru 20 da ke zaune a birnin Ikko, a kotun Tarayyar da ke Grand Rapids gobe Litinin.

Jordan DeMay (DeMay family)
Jordan DeMay (DeMay family)

Ana zargin matasan ne da kafa wata kungiyar damfara da tilasa kananan yara a kasashen duniya biyan toshiya, da karyar cewa, su mata ne, da hakan ya yi sanadin mutuwar wani matashi dan shekaru 17 mai suna Jordan DeMay dake da zama a Marquette, a yankin Upper Peninsula, wanda ya yi amfani da bindiga ya harbe kanshi har lahira ranar 22 ga watan Maris na shekara ta 2022.

Ana tuhumar kowane dayansu da laifin hada baki da tilasta wa kananan yara biyan kudin toshiyar abin fallasa, da hada baki su yada hotunan batsa da kananan yara ta yanar gizo, da hada baki su rika bin kananan yara sau da kafa ta yanar gizo.

Jordan DeMay (DeMay family)
Jordan DeMay (DeMay family)

Banda haka kuma, ana zargin Samuel Ogoshi da laifin lalata da kananan yara da ya yi sanadin rasa rai.

An tuhumi matasan biyu ne da aikata laifukan a nan Amurka a watan Mayu, duk da yake wadanda ake tuhuman suna Najeriya. Daga nan hukumomi suka shiga daukar matakan bin sawun sadarwar ta yanar gizo da ya kai ga gano inda wadanda suka aikata laifin suke da kuma ainihin wadanda suka aikata laifin .

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun yi zargin cewa, wadanda ake tuhuman sun sayi wani shafin sadarwar internet da aka yi wa kutse, suka yi amfani da shafin wajen nuna cewa su mata ne domin rinjayar samari wajen yin zance irin na lalata. Daya daga cikin shafukan sada zumuntan da su ka yi amfani da su, sunansa “dani.robertts”, inda suka yi amfani da shi wajen yin hira da DeMay kafin mutuwarshi.

Jordan DeMay (DeMay family)
Jordan DeMay (DeMay family)

Mutanen da ake zargi sun rika amfani da hanyar bincike ta yanar sadarwar “Google” da wadansu hanyoyin sadarwar zamani wajen gano ainihin inda mutanen da suke razanawa su biya toshiya din ke zaune, da inda suka je makaranta, da inda suke aiki da kuma inda danginsu ko abokansu ke zaune.

Bisa ga cewar masu taimaka wa hukuma tantance laifin, daga nan sai wadanda ake tuhuman su rika sa mutane daukar hotunan batsa suna tura masu. Da zarar sun sami hotunan sai su tattara su wuri daya su hada da hotunan mutane da suka tattaro a shafukan sada zumunta dabam dabam da ya hada da hutunan makarantarsu da kuma na danginsu da abokansu. Jami’an sun ce mutanen da ake tuhuma sun tozarta sama da mutane 100 tare da neman kudin toshiya ta wannan hanyar.

Jordan DeMay (DeMay family)
Jordan DeMay (DeMay family)

Bisa ga jami’ai, Samuel Ogoshi ya yi amfani da shafin sada zumunta mai suna dani.robertts rana 25 ga watan Maris 2022, bayan da suka rudi DeMay ya tura masu hotonshi tsirara, sannan ya yi masa baraza don ya biya toshiya.

A hirar ta da tashar talabijin ta TV6 mahaifiyar DeMay ta ce bata taba yin tsammanin hukumomi za su iya kamowa da kuma hukumta wadanda su ka yi sanadin mutuwar danta ba, ta ce, Hukumomi sun yi daidai da suka tasa keyarsu zuwa Amurka domin amsa laifinsu.

https://www.justice.gov/usao-wdmi/pr/2023_0503_Sextortion_Indictment

Idan aka same su da laifi, Samuel Ogoshi yana iya fuskantar daurin rai da rai, yayinda kaninshi, Samson ke fuskantar hukumcin daurin shekaru 55 a gidan yari.

A farkon wannan shekarar jami’an Hukumar FBI suka tafi Najeriya domin gudanar da bincike na hadin gwiwa da jami’an tsaron Najeriya da ya yi sanadin kama Samuel Ogoshi da Samson Ogoshi kafin aka tasa keyar su zuwa Amurka yayinda ake jiran lokacin tasa keyar Ezekiel Ejehem Robert dan shekaru 19.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG