Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanar Da ‘Yan Najeriya Biyu Da Ake Tuhuma Da Tursasa Wa Wani Matashin Ba’Amurke Da Ya Kashe Kansa


Samson da Samuel Ogoshi
Samson da Samuel Ogoshi

Wata kotu a Amurka ta gurfanar da wasu ‘yan Najeriya biyu da ake tuhuma da laifin tursasa ma wani matashin ba’Amurka har ya kashe kansa; da kuma laifin zambatar dinbin Amurkawa, da tilasta su biyan kudin toshiya ta wajen masu barazanar tonon silili mai nasaba da lalata.

Matashin mai suna Jordan DeMay, mai shekaru 17, ya kashe kansa ne biyo bayan kasa biyan kudin toshiyar da wadannan ‘yan Najeriyan su ka yi barazanar sai ya biya ko kuma su bayyana ma duniya abin fallasar da ya yi, alhalin kuwa su ne su ka yaudare shi ya yi abin fallasar ta batsa.

Jami'an FBI Suna gabatar yiwa manema bayani
Jami'an FBI Suna gabatar yiwa manema bayani

Ana tuhumar matasan, Samuel Ogoshi da Samson Ogoshi, wadanda aka taso keyarsu daga jihar Nasarawa ta Najeriya zuwa Amurka, da kafa wata kungiyar zamba ta kafar sadarwa, inda su ke amfani da hotunan kyawawan ‘yan mata da su ka kofo ta intanet, su yaudari mutane da su.

Da yake karin bayani ga manema labarai bayan zaman kotun, jami’in hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a jihar Michigan Devin Kowalski Ya ce, "wannan bincike ne da ya shafi bangarori da dama. Ya shafi ganowa da tantance daruruwan mutane da laifin ya shafa, bin sawun da wadanda ake tuhumar su ka bari a hanyar sadarwar internet, bin sawun kudaden da wadanda suke tsorawa da tilasa masu biyan toshiya su ke biya ta cibiyoyi da hanyoyin tura kudi, da kum aiki da ofishinmu a Najeriya da kuma abokan huldarmu na Najeriya."

Akwai kuma mutum na uku da ba a kai ga taso keyarsa ba tukunna.

Jordan DeMay(DeMay family)
Jordan DeMay(DeMay family)

Wannan ne karon farko da iyayen Jordan suka hada ido da matasan da suka zambaci dansu. Zaman gabatar da karar ya kasance wani zama mai sosa rai, inda iyayen yaron su ka yi ta hawaye, yayinda wadanda ake tuhumar suka nuna matukar kaduwa, da daya daga cikinsu ya yi ta rawar jiki. Sun yi ta amsa tambayoyin alkalin da 'I" ko "A'a" kawai lokacin da yake karanta laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

an-mika-hushpuppi-dan-najeriyar-da-ake-zargi-da-damfara-zuwa-ga-fbi-

amurka-ta-yanke-wa-wani-dan-najeriya-hukuncin-daurin-shekaru-four-saboda-damfara-ta-intanet

Wannan karar ta zama zakaran gwajin dafi a tuhumar irin wannan laifin, kasacewa, duk da yake laifin kutse a hanyar sadarwar yanar gizo da kuma zambatar al'umma ya zama ruwan dare, da Najeriya ta kasace daya daga cikin kasashen da suka yi kaurin suna a aikata irin wannan laifin, ya kasance karon farko da ake tasa keyar masu aikatar laifin zuwa Amurka domin fuskantar shari'a.

Ranar Alhamis za a ci gaba da shari’ar bayan da kotu ta samar wa mutanen da ake tuhumar da lauyoyin gwamnati da za su kare su.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG