WASHINGTON, D.C. - NIGERIA - Kungiyar ta masu aikata laifuka da ke aiki a kasashen Najeriya da Malesiya, da dai sauran wurare, wadanda suka aiwatar da zamba ta hanyar amfani da yanar gizo.
A cewar takardun kotu, tsakanin watan Disamba na 2011 zuwa Janairun 2017, Solomon Ekunke Okpe tare da abokansa da suka aikata laifin, sun kirkiri wata hanyar damfara ta amfani da hanyar imel na kasuwanci (BEC), na aiki-daga gida, da fidda kudi ta amfin da check din banki, soyayya, katin banki don damfarar mutane da ba su ji ba basu gani ba, bankuna, da masana’antu a Amurka da sauran wurare, wanda yin hakan zai haddasa asarar fiye da dala miliyan daya ga Amurkawa da wadanda lamarin ya shafa. Cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da kamfanin First American Holding, da bankin MidFirst.
Okpe da abokansa sun kaddamar da hare-haren satar bayanan sirri na imel don satar muhimman bayanan mutane, da yin kutse ta yanar gizo, don aiwatar da damfarar, suka rika yin amfani da bayanan suna damfarar mutane, bankuna, masana’antu, sun kuma yi safarrar, da amfani da katunan banki da aka sace don ci gaban damfararsu.
Okpe da hadakarsa sun kuma gudanar da zamba ta hanyar soyayya ta shafukan soyayya na yanar gizo, da nuna sha’awar mu’amalar soyayya da mutane da sunayen karya, don mutane su tura musu kudade zuwa ketare ko zamba ta hanyar waya. Okpe ya sa dubban mutanen sun fuskanci asarar dubban daloli ta hanyar soyayya.
A baya dai an kama Okpe a Malaysia bisa bukatar Amurka kuma an tsare shi sama da shekaru biyu a lokacin bayan da ya nemi a mika shi ga Amurka.
A ranar 20 ga Maris, aka yanke wa daya daga cikin wadanda suka hada baki da Okpe, Johnson Uke Obogo, hukuncin daurin shekara daya da kwana daya a gidan yari, dangane da rawar da ya taka wajen zambar kudade.
Hukumar FBI ta gano adadin wadanda abin ya shafa, duk da haka, akwai wadanda har yanzu ba a tantance su ba.