Wannan na daga cikin sauye sauyen da shugaban kasar Yarima Mohammed bin Salman ya yi wanda yake kokarin gudanar da canje canje a masarautar ya kuma bada dama a kasar da ke dogaro ga albarkatun man fetir.
Tun hawan shi mulki, aka ba mata damar tuka mota da tafiya kasashen waje ba tare da dan rakiya namiji ba, duk da kuntatawa masu kushewa mulkinshi da hukumomi ke yi da suka hada da ‘yan gwaggwarmaya mata.
‘Yan asalin kasar Saudiya dubu sittin da aka zaba ta hanyar tambola ne kadai zasu gudanar a ayyukan hajji bana. Jami’ai sun ce kashi 40% cikin dari na wadanda za su gudanar da aikin hajjin bana, mata ne.