Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Saudiyya Ta Ce Za Ta Tallafawa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka


Yarima Salman na kasar Saudiyya
Yarima Salman na kasar Saudiyya

"Saudiyya ta kashe kusan dala biliyan hudu a fannonin samar da wutar lantarki, fasahar sadarwa, samar da abinci a nahiyar Afirka."

Saudiyya za ta tallafawa kasashen nahiyar Afirka ta hanyar saka hannayen jari da ba ta bashin dala biliyan daya domin a farfado tattalin arzikin nahiyar da ya tagayyara sanadiyyar annobar COVID-19, Yarima Mohammed Bin Salman ya ce.

“Gidauniyar ba da tallafi ta Saudiyya za ta gudanar da wasu ayyukanta da ba da bashi har na riyal biliyan uku wajen bunkasa kasashen Afirka a wannan shekara,” Yarima Salman ya fada yayin wani jawabi da ya yi ta talabijin ga taron da aka yi a Paris don tallafawa kasashen nahiyar.

Ya kara da cewa, Saudiyya ta kashe kusan dala biliyan hudu a fannonin samar da wutar lantarki, fasahar sadarwa, samar da abinci a nahiyar Afirka, kuma za ta ci gaba da duba wasu fannoni da za ta taimakawa nahiyar.

A farkon makon nan, shugabannin kasashen duniya da manyan hukumomin ba da lamuni na suka hallara a birnin Paris, domin lalubo hanyoyin da za su samawa nahiyar ta Afirka kudaden da za su farfado da tattalin arzikin nahiyar, wanda ya maku da annobar coronavirus.

Sannan an tattauna kan yadda za a shawo kan dumbin basukan biliyoyin daloli da ake bin kasashen nahiyar.

Akalla shugabannin kasashen Afirka da na nahiyar turai 30 ne suka halarci taron, hade da shugabannin manyan hukumomin sarrafa kudade kamar IMF da bankin duniya.

XS
SM
MD
LG