Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya Ta Ce Zata Kulla Dangantaka da Isira’ila Ne Kawai Idan An Samu Zaman Lafiya Isira'ilar da Falasdinawa


Sarki Salman
Sarki Salman

Kasar Saudiyya ba ta kau da yiwuwar kulla dangantaka da kasar Yahudu ba, to amma ta ce sai kasar ta Isira'ila ta daidaita da Falasdinawa tukun.

Saudiyya, kasar Larabawa mafi tasiri a duniya, kuma inda nan ne masallatai mafiya daraja a addinin Musulunci suke, ta bayyana matsayinta a hukumance kan dadaddiyar takaddamar nan ta Gabas Ta Tsakiya. Matsayin tan kuwa shi ne: za ta kulla cikakkiyar dangantaka da Isira’ila ne kawai, idan aka samu zaman lafiya tsakanin Isira’ilar da Falasdinawa.

Duk da haka dai, kafafen yada labaran gwamnatin Saudiyya da kuma wasu malamai na nuna alamar sauyi na nan tafi a dangantaka da Isira’ila – wanda hakan na iya faruwa ne kawai bisa umurnin Yarima Mai Jiran Gado, mai matukar tasiri, Muhammad bin Salman.

Wadannan sakonnin da ke cin karo da juna, game da yiwuwar kulla dangantaka tsakanin Saudiyya da Isira’ila, na nuni da abin da masu lura da al’amura da kuma ‘yan ciki ke cewa, hannun riga ne tsakanin yadda yariman, mai shekaru 35, da kuma mahaifinsa, mai shekaru 84, Sarki Salman, ke fassara muradun kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG